Hukumar ICPC ta ce da ana aiwatar da dokokin yaƙi da cin hanci da rashawa yadda ya kamata, da kusan kashi 80 na ’yan Najeriya na ɗaure a gidan yari.
Kwamishinan ICPC na Jihar Kaduna, Sakaba Ishaku ne, ya bayyana haka a wani taron horaswa kan yadda ake kula da amana a ƙananan hukumomi.
Kwamishinan ICPC na Jihar Kaduna, Sakaba Ishaku ne, ya bayyana haka a wani taron horaswa kan yadda ake kula da amana a ƙananan hukumomi.
Ya ce cin hanci ya yi tasiri sosai a rayuwar ’yan Najeriya, kuma yana haifar da talauci, rikice-rikice, da jinkirta ci gaban ƙasa.
Ya ƙara da cewa yawancin dukiyar da wasu ke taƙama da ita a Najeriya ma da alaƙa da aikata rashin gaskiya, kuma mutane da yawa ba sa son jin batun yaƙi da cin hanci saboda suna jin daɗin aikata shi.
- Gwamna Bala Abdulkadir Ya Musanta Zargin Shirin Sauya Sheka Daga PDP Zuwa PRP
- Sojojin Nijeriya Sun Kashe ƙasurgumin ɗan bindiga Kachalla Kallamu
Ishaku, ya soki shugabannin ƙananan hukumomi da ke barin kujerarsu ba tare da sun aiwatar da wani gagarumin aiki ba.
Ya kuma nemi a tsaurara hukunci ga masu satar dukiyar gwamnati, inda ya ce duk wanda ya saci dukiyar jama’a bai kamata a masa hukunci mai sauƙi ba.
Kwamishinan Harkokin Ƙananan Hukumomi na Kaduna, Sadiq Mamman Legas, ya goyi bayan bayanan ICPC.
Ya ce gwamnati ta gyara na’urorin wutar lantarki a wasu yankuna, amma mazauna wajen suka lalata, tare da suka sace wasu.
Ya ce ba za a samu ci gaba ba idan mutane suna lalata dukiyar gwamnati.
Dukkanin jami’an sun yi kira da a ƙara ƙarfafa doka, a kula da ayyukan gwamnati sosai, kuma a wayar da kan jama’a domin rage cin hanci da kare kayayyakin gwamnati.
