Shugaban ƙaramar hukumar Kabo dake Kano kwamared Lawal Na Jume ya saya wa jama’ar garin Gabasawa filin maƙabarta da aka daɗe ana buƙata a yankin.
An saya wa jama’ar yankin Gabasawa filin maƙabartar ne da yammacin ranar Alhamis 21 Ga Nuwamba 2024 akan Naira miliyan daya da dubu ɗari biyar, kamar yadda sakataren mulkin ƙaramar hukumar Kabo honorabul Abba Salihu mai wake Garo ya bayyana.
- Sanata Barau Ya Bai Wa ‘Yan Sanda Babura Dubu 1 A Kano
- Yadda Mai Hannu 1 Ke Samun Dubu 3 Kullum A Sana’ar Faskare
Yayin biyan kuɗin maƙabartar, shugaban ƙaramar hukumar Kabo kwamared Lawal Na Jume ya samu rakiyar mataimakinsa honorabul Kabir Lawal da kuma sakataren mulkin ƙaramar hukumar honorabul Abba Salihu mai wake Garo.
An damƙa filin maƙabartar ne da hannun babban limamin Gabasawa da kuma Dagacin yankin.
Bayan biyan kuɗin maƙabartar, limamin garin da wasu dattawa da aka gayyata domin shaida cinikin sun bayyana farin cikinsu da tallafin filin maƙabartar da suka samu daga shugaban ƙaramar hukumar.