Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Sanata Barau I. Jibrin, ya bai wa Rundunar ’Yan Sandan Kano, kyautar babura guda 1,000.
Taron bayar da tallafin ya gudana ne a ranar Asabar a hedikwatar ’yan sandan da ke Bompai a Kano.
- Yadda Mai Hannu 1 Ke Samun Dubu 3 Kullum A Sana’ar Faskare
- An Sace Mai Anguwa Da Wasu Mutane 11 A Kaduna
Sanata Barau ya bayar da tallafin ne domin taimaka wa jami’an ’yan sanda, wajen inganta ayyukansu da kuma tabbatar da tsaro a jihar Kano.
An ƙera baburan ne don yin aiki a kowane irin yanayi.
Ko a bara (shekarar 2023), Sanata Barau ya bai wa rundunar ‘yan sandan motocin aiki guda 22 domin tallafa wa ayyukantaa jihar.