Wani ɗan kimanin shekara 40 mai hannu ɗaya da ke sana’ar faskaren itace a garin Kafanchan jihar Kaduna na ci-gaba da ɗaukar hankalin mutane.
Ganin cewa, wasu masu hannuwa da ƙafafu na zaman jiran gwamnati ko mawadatan anguwanninsu ko ‘yan uwansu su basu, amma wannan matashin dattijon da ke da hannu ɗaya, ya zaɓi ya yi faskare domin ɗaukar nauyin kai da kai.
Sunday Bulus ya bayyanawa manema labarai cewa “mutane da dama suna mamaki a duk lokacin da suka fara ganina a karon farko ina faskaren itace da hannu ɗaya.
“A sanadiyyar haka ma na sha samun kyaututtuka daban-daban daga mutane iri-iri da suke cewa ina burge su,”
“A haka nake samun mutane iri daban-daban dake tausaya min ganin irin halin da nake ciki na lalura amma hakan bai kashe min zuciya ba.”
- An Sace Mai Anguwa Da Wasu Mutane 11 A Kaduna
- Gwamnatin Jihar Kano Ta Ƙuduri Aniyar Farfaɗo Makarantun Kimiya Da Fasaha
Sunday Bulus, ɗan asalin Unguwar Bayan Loko ne da ke yankin Kafanchan ya bayyana cewa shekararsa ɗaya ke nan da farawa.
“kamar wasa wani ya tsokane ni ko zan iya yi masa faskare a gidansa in zo in yi zai biya ni.
“Na ce masa ƙwarai kuwa mai zai hana, ban taɓa yi ba, amma na amsa masa kuma na je na yi masa tsaf, nan take ya biya ni ya kuma buƙaci na ci gaba da zuwa ina yi yana biya na.
“Daga nan na samu sana’ar yi, aiki ya kankama inda wasu suka fara kira na, musamman masu sayen itatuwa don su faskara su siyar”.
Sunday ya ce ya kan yi faskaren Naira dubu uku a rana idan akwai aiki, don ba kullum ake samun aikin ba.
Ya ce iyakar karatunsa ya tsaya ne a karamar sakandare inda ya kammala aji uku amma bai samu damar ci gaba da karatu ba saboda rashin mai ɗaukar nauyinsa.