Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ƙaddamar da sabon ofishin ’yan sanda da aka gina a garin Falgore, da ke ƙaramar hukumar Rogo.
An gudanar da bikin ƙaddamar da ofishin ne tare da halartar Kakakin majalisar dokokin jihar Kano, Rt. Hon. Jibril Ismail Falgore, shugaban ƙaramar hukumar, sarakunan gargajiya da sauran al’umma.
CP Bakori ya ce gina ofishin na daga cikin ƙoƙarin samar da tsaro a matakin al’umma da kuma kusantar da ayyukan ’yan sanda ga jama’a, kamar yadda Sufeto Janar na ’yan sanda, IGP Olatunji Rilwan Disu, ke fata.
Ya bayyana cewa ofishin na da kayan aiki na zamani, ciki har da ɗakunan gudanarwa, wurin karɓar ƙorafe-ƙorafe, ɗakin tsare waɗanda ake zargi da kuma masaukin jami’ai.
Kwamishinan ya buƙaci jami’an da za su yi aiki a ofishin su kasance masu ƙwarewa da biyayya ga doka, tare da girmama haƙƙin jama’a, yana mai gargaɗin cewa ba za a lamunci cin hanci ko karɓar kuɗi ba bisa ƙa’ida.
A nasa jawabin, Kakakin majalisar dokokin Jihar Kano, Jibril Ismail Falgore, ya ce ya gina ofishin ne domin ƙara ganin ’yan sanda a yankin da kuma magance matsalolin tsaro.
Ya kuma yi kira ga al’ummar yankin da su ba jami’an tsaro haɗin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai domin yaƙi da laifuffuka.