Kwalara na daya daga cikin ƙwayoyin cututtuka da suke yaduwa ta hanyar ruwa, ko ta abinci maras tsafta.
Kwalara na haifar da amai da gudawa, kuma tana saurin yin kisa idan har ba a ɗauki mataki a kan lokaci ba.
Waɗanda cutar ta yi wa tsanani za su yi fama da rashin ruwan jiki wanda zai kai ga haddasa babbar matsala kuma idan ba a yi gaggawar magani ba mutum na iya rasa ransa.
A cikakken bayanin da CDC ta yi kan kwalara ta ce kusan mutum miliyan uku ke kamuwa da cutar duk shekara kuma tana kashe mutum 95,000 duk shekara a duniya.
Ana iya kamuwa da cutar ba tare da nuna wani alamomi ba, Alƙalumman CDC sun nuna cewa mutum ɗaya cikin goma da suka kamu da cutar kwalara za ta iya yin tsanani da nuna alamu na amai da gudawa sosai da kuma mutuwar jiki.
Cutar kwalara ta kara barkewa a jihar sokkwato wanda tayi sanadiyyar mutuwar mutum 25 a Jihar inda ta shafi kananan hukumomin Sakkwato ta Arewa, Kware da Silame.
Kwamishinar Lafiya ta Jihar, Hajiya Rabi Balarabe ce, ta tabbatar da cewa mutum 1,160 ne suka kamu da cutar, yayin da 15 ke kwance a asibiti suna karbar magani.
Matsalar ta fi tsanani a Bazza Gidadawa da ke Karamar Hukumar Sakkwato ta Arewa.
Gwamnatin jihar ta samar da magunguna kyauta ga yankunan da abin ya shafa tare da daukar ma’aikatan jinya 864 don bunkasa bangaren lafiya.
Hanyoyin kare kai
Kamar yadda Hukumar daƙile yaɗuwar cutuka ta Najeriya ta bayyana, hanyoyin kare kai daga kamuwa da kwalara su ne:
Shan ruwa mai tsafta.
Tsaftace muhalli.
Zubar da shara a wurin da ya kamata.
Tsaftar jiki ta hanyar wanke hannu da sabulu da ruwa mai gudana.
Ƙaurace wa shan kayan zaƙi (Zoɓo ko Jinja) da babu tabbas kan tsaftar su.
Ƙaurace wa shan kayan marmarin da ake sayarwa a kan titi ba tare da rufewa ba, musamman waɗanda aka fere kamar kankana da abarba.
Guje wa cin abincin da ba a dafashi yadda ya kamata ba.
Likitoci da hukumomin lafiya suna ba da shawarwari akan baiwa masu cutar ruwan gishiri da suga da agorar ruwa mai tsabta lita ɗaya a bai wa wanda ya harbu da cutar ya sha.
Idan kuma cutar ta yi ƙamari, a garzaya da mutum mafi kusa domin a yi wa mutum ƙarin ruwa.
Idan kuma jariri ne ya harbu da cutar, ana bawa mahaifiyar shawara ta ci gaba da shayar da shi ruwan nono.hakan zai taimaka masa matuka gurin yakar cutar.