Home » Ba Tsoron Gwamnonimu Mu Ke Ji Ba…-Sarkin Musulmi 

Ba Tsoron Gwamnonimu Mu Ke Ji Ba…-Sarkin Musulmi 

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment
Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III, Ya Shawarci Al’umma da Su Fara Duban Watan Babbar Sallah

Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya musanta zargin da ke cewa sarakunan gargajiya suna tsoron gwamnonin jihohinsu.

Sarkin ya bayyana cewa sarakunan gargajiya sun daɗe suna mulki tun kafin samun ’yancin kai a Najeriya, kuma suna da cikakkiyar fahimta game da ƙasa sama da shuwagabannin da ke rike da jihohin a yanzu.

Mai Alfarma ya yi wannan bayani ne a taron tattaunawa kan cigaban matasan Arewacin Najeriya, da Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello ta shirya a Abuja ranar Talata.

Jawabin na sarki martani ne, ga kalaman tsohon Gwamnan Jihar Neja, Masu Babangida Aliyu, wanda ya ce sarakunan gargajiya suna tsoron gwamnoni.

Sarkin ya ce, “Na ji wasu suna cewa sarakunan gargajiya suna tsoron gwamnonin jihohi. Wannan ba gaskiya ba ne.

“Sarakunan gargajiya kawai suna mutunta kansu ne da kuma mutunta gwamnonin, waɗanda ke da iko a jihohinsu. Ba wai tsoro ba ne.

“Idan wani abu ya faru, muna barinsa ga Allah Mai iko a kan komai. Muna karɓar duk wani sauyi da ya zo.

“Kafin a samu gwamnonin jihohi, sarakunan gargajiya sun riga sun fara mulki a wuraren da suka zama Najeriya tun daga 1914, kafin samun ’yancin kai a 1960.

“A matsayinmu na shugabannin gargajiya, muna da kusanci sosai da al’ummarmu saboda mun san buƙatunsu, kuma muna tare da su duk lokacin da wani abu ya faru.”

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?