Home » Matsayar Malaman Addinin Musulunci A Najeriya Dangane Da Kudurin Haraji

Matsayar Malaman Addinin Musulunci A Najeriya Dangane Da Kudurin Haraji

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Majalisar Malaman Addinin Musulunci ta Najeriya ta bayyana matsayar ta dangaen da kudurin yi wa dokar harajin Najeriya gyran fuska.

A wata sanarwa da majalsair malaman addinin Musulunci ta Najeriya ta fitar a ranar Litinin 18 ga Nuwamba, 2024, ta bukaci shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da kudurin yi wa dokar haraji gyaran fuska. 

Majalisar ta yi bitar kundin kudurin dokar, da kuma halin da Najeriya ta tsinci kanta tun bayan bayyanar kunshin gyaran fuskar da shugaba Tinubu ke shirin yi. 

Malaman Sun bayyana cewa a sabon tsarin, mafi yawan kuɗaɗen haraji da za a riƙa tarawa, wasu tsirarun jihohi ne za su fi cin moriya.

“Ƙudurin gyara haraji na Tax Reform Bills, musamman na Nigeria Tax Bill (NTB), 2024 da na Nigeria Tax Administration Bill (NTAB) 2024 babu daidaito a ciki,” in ji sanarwar.

“Ƙudurin NTAB zai sa a riƙa kwashe mafi yawan harajin VAT da aka tara a jihohi zuwa jihohin da shalkwatar kamfanonin suke. Wannan tsarin ya saɓa ƙa’idar samar da daidaito, domin duk kayayyakin da kamfani ke yi, ba su da amfani matuƙar babu masu amfani da su.

“Babu adalci a ciki saboda masu biyan harajin ba za su ci moriyar kuɗaɗen da suke biya ba, wanda hakan ya saɓa da ƙa’idar karɓar haraji kamar yadda yake a ƙunshe a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.

“Sannan a sabon tsarin na NTB, za a rufe wasu muhimman ɓangarorin gwamnati kamar TETFUND da NITDA, wanda su ne ke taimakawa wajen samar da ababen more rayuwa da tallafin karatu.”

‘Abubuwan da muka lura a cikin ƙudurin’

Majalisar malaman ta kuma zayyano wasu abubuwa da ta ce ta gano suna ƙunshe a cikin ƙudurorin, waɗanda a cewarta suka sa ta yi fatali da gyare-gyaren.

“Ƙudurin na NTB 2024 da na NTAB 2024, za su tattara wasu haraji masu kusanci su zama ɗaya. Sai dai matsalar ita ce, jihohin da shalkwatar kamfanonin suke, su ne za su fi cin moriyar kuɗaɗen da aka tara, maimakon jihohin da masu amfani da kayayyakin suke.

“Ƙudurorin za su fi amfanar jihohi uku, sama da sauran jihohin ƙasar, wanda hakan zai shafi tattalin arzikinsu.”

Majalisar ta ƙara da cewa ɓullo da garambawul ɗin a wannan lokacin da ake fama da tsadar rayuwa a Najeriya ba daidai ba ne, sannan ta ƙara da cewa ƙudurin NTB zai sa a rage kuɗaɗen da ake bai wa asusun tallafa wa ilimi na TETFUND da NITDA da NASANI maimakon kashi 4 na ribar kamfanonin a 2025 da 2026 zuwa kashi 2 a 2030.

“Idan aka hana hukumomin samun kuɗaɗe da suke samu daga asusun development levy, da wahala su cigaba da aiki ko da kuwa suna samun kuɗi daga gwamnatin tarayya,” in ji majalisar malaman, sannan suka ƙara da cewa hakan zai shafi harkokin TETFUND sosai.

“Wannan zai so dole makarantun su nemi wasu hanyoyin samun kuɗaɗe domin inganta makarantu da bincike-bincike da ɗaukar nauyin malamai domin ƙaro karatu da sanin makamar aiki, wanda hakan zai sa dole makarantun su ƙara kuɗin makaranta.”

Abin da ya kamata a yi

Malaman sun kuma bayyana cewa sun yi nazarin ƙudurorin da abubuwan da za su biyo baya, musamman ga jihohin da suke zargin za a danne, inda suka ce lallai akwai buƙatar gwamnatin tarayya ta saurari buƙatar majalisar tattalin arzikin ƙasar.

“Wannan zai sa a fahimci juna sannan su dace da dokokin ƙasar tare da wanke zargin cewa bankin duniya da bankin bada lamuni ne suka ƙaƙaba wa Najeriya su,” in ji sanarwar majalisar, sannan ta bayar da shawarwari kamar haka:

Ya kamata gwamnoni su nemi shawarwari daga masana domin a yi nazarin ƙudurorin sosai.

Gwamnonin su buƙaci a dakatar da aiwatar da ƙudurorin a yadda suke a yanzu ba tare da an yi gyara ba.

A bayar da damar nazari tare da muhawara a kan ƙudurori.

Ƴan majalisar dokoki su yi abin da ya kamata wajen ƙin amincewa da ƙudurorin da za su cutar da waɗanda suke wakilta

Dukkan ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun mutane su fito bayyana rashin amincewarsu da tsarin.

A ƙarshe majalisar malaman ta Ulama Forum ta ce, “muna kira da a janye ƙudurorin, a koma teburin tattaunawa domin a samu matsaya mai kyau.”

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?