Home » Dakarun Sojin Hadin-gwuiwa da Najeriya Sun Kashe Wasu Mayakan Boko Haram

Dakarun Sojin Hadin-gwuiwa da Najeriya Sun Kashe Wasu Mayakan Boko Haram

by Anas Dansalma
0 comment
Dakarun Sojin Hadin-gwuiwa Ta Ƙasashen Afirka Sun Kashe Mayakan Boko Haram

Dakarun rundunar soji ta hadin-gwuiwa da aka fi sani da Multinational Joint Task Force da ke aiki a yankin Tafkin Chadi sun yi nasarar kashe mayakan Boko Haram tare da ƙwace makamai masu yawa.

Wannan na zuwa ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar haɗin gwuiwar, Kanal Kamarudeen, ya fitar jiya, ta ce dakarun sun samu wannan nasara ne karkashin shirin nan na Operation Harbin Kunama.

Sanarwar ta ce dakarun rundunar sojin ta kashe ‘yan Boko Haram da dama, sai dai ba ta bayyana adadinsu ba.

Haka kuma sanarwar ta ce rundunar ta kai wani samame a yankin Ferondiya da ke yankin Tafkin Chadi inda ta tarwatsa maboyar ‘yan ta’adda.

Rundunar ta MNJTF ta ce ta kwato a-kori-kurar da ake
girke bindiga da kuma bindigar harbo jirgin sama biyu da makamin RPG da AK 47 biyu da bam din RPG da motoci uku kirar Toyota da ake girke bindiga.

Rundunar ta Multinational Joint Task Force ta kunshi dakaru daga Nijeriya da Nijar da Kamaru da Benin da Chadi inda kuma hedikwatar rundunar take a Chadi.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?