Home » Dalilin Da Yasa Bamu Fara Biyan Ƙarin Alawus Ba – NYSC

Dalilin Da Yasa Bamu Fara Biyan Ƙarin Alawus Ba – NYSC

by Mubarak Ibrahim Mandawari
0 comment

Bayan gaza fara biyan masu yiwa ƙasa hidima ƙarin Alawus na Naira 77,000, hukumar yi wa ƙasa hidima ta Najeriya NYSC ta ce dalilin ƙin biyan kuɗin baya rasa nasaba ne da rashin sakar musu ƙarin kudin da gwamnatin tarayya bata yi ba.

Shugaban hukumar NYSC Birgediya Janar Yush’au Dogara Ahmad ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da ya yi da mena ma labarai.

Shugaban hukumar ya ƙara da cewa a hukumance sun samu takardar amincewa da ƙarin, amma ba’a riga an sakar wa hukumar kuɗin ba.

“Ba iya masu yiwa ƙasa hidima ba, har ma’aikatan hukumar mu suma an yi musu ƙarin, su nasu ya kai wata hudu zuwa biyar, amma har yanzu ba’a fara biyan suba” a cewar shugaban.

“Muna sa ran nan bada daɗewa ba za’a fara biyan wannan ƙarin da akayi na sabon albashi.”

”Bayanin da muka samu ba a ce mana ga ranar da za’a fara biya ba, amma dai an tabbatar mana cewa an yi musu ƙarin daga ranar 29 ga watan Yulin 2024”

Cikin sanarwa da hukumar ta fitar ta ce ƙarin sabon alawus ɗin zai fara aiki ne daga watan Yulin wannan shekarar, abin da ke nuna cewa masu yi wa ƙasa hidimar za su samu ariyas na aƙalla watanni uku.

To sai dai da dama daga cikin masu hidimar ƙasar sun saka rai da ganin ƙarin  alawus ɗin a watan da ya gabata.

Masu yi wa ƙasa hidima sun koka kan yadda tsadar kayan masarufi ke jefa su cikin wani hali, kuma a baya sun yi roƙo akan suna buƙatar a ɗauki mataki domin tafiyar da al’amuran su na yau da kullum.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?