Dan Jaridar Al Jazeera Ya Rasa Ransa A Harin Isra’ila A Gaza

Daga : Shareep Khaleepha Sharifai

Isra’ila ta kaddamar da sabbin farmaki kan zirin na Gaza a kokarinsu na murkushe mayakan Hamas tare kuma da kwato ragowar fursunonin yakin kasar da ke hannun mayakan.Sabbin hare-haren da Isra’ila ta kaddamar a zirin Gaza ya halaka wani ‘dan jaridar Al Jazeera Hussam Shabat, yayinda sojojin Isra’ila suka bukaci fararen hula da su fice daga shiyyar arewacin Gaza a ci gaba da luguden bama-bamai ta sama a yankin.Mai magana da yawun rundunar tsaron Isra’ila Avichay Adraee ya ce sun aike da sako ga daukacin al’ummar yankin na Gaza kan bukatar ficewa kafin kaddamar da sabbin hare-haren kan birnin Jabalia.Hukumomin tsaron Gaza sun ce harin da Isra’ila ta kai da jirgi maras matuki shi ne ya yi sanadiyyar mutuwar ‘dan jaridar na Al Jazeera Mubasher, Hussam Shabat a kusa da wani gidan mai da ke Beit Lahia. Kwamitin da ke kare ‘Yan Jarida na kasa da kasa da ke Amurka ya fitar da wani rahoto dake cewa a watan Oktobar 2024, Isra’ila ta zargi Shabat da wasu ‘yan jarida biyar da taimakawa ‘yan ta’adda, zargin da ya Shabat din ya musanta.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda