Kwamishinan Tsaro Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa A Kano

Daga Safiyanu Haruna Kutama

Kwamishinan kula da harkokin tsaro da al’amuran cikin gida na Jihar Kano, Manjo Janaral Muhammad Inuwa Idiris (mai ritaya), ya ajiye aikinsa.

Wata sanarwar da mai magana da yawun gwamnan Jihar Kano, Alhaji Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ta bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kadu da matakin da kwamishinan ya dauka.

Gwamnan ya kuma mika sakon godiya ga Manjo Janaral Inuwa Idiris bisa gudunmowar da ya bayar wajen tsare lafiyar al’umma da tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnan ya karbi takardar ajiye aikin kwamishinan nan take, duk da cewa bai bayyana dalilan yin hakan ba.

Post masu alaƙa

Gwamnatin Jigawa ta kashe kusan naira biliyan bakwai (7) domin tallafa wa ma’aikata ta fuskar noma

Jami’an tsaro sun ceto ɗalibai da malaman da aka sace a Kogi

Hukumomin tsaro sun kama wanda ya kirkiri hukumar bogi a Nijeriya