Dan takarar da ake zargin ya yi wa yar shekara 13 ciki a Katsina ya kai Hisba kara.

Dan takarar da ake zargi  ya yi wa yar shekara 13 ciki a Katsina ya kai Hisba Kara, a cikin cikin wani faifan bidiyon da Hukumar Hisba ta Jihar Katsina ta fitar, an ga wani Jami’an Hukumar Hisbar yana tambayar wata mata cewa, inda ‘yarta ce aka yi wa fyade ta yi ciki har ta haihu za ta iya zuwa ta fada wa hukumar an yi sasanci?

Jami’in Hisbar ya kuma yi bayanin cewa, a baya bayan sun kama wanda ake tuhumar, kuma shi da kansa ya amsa cewa, shi ya yi wa yarinyar ciki kuma ya amince zai aureta a wani mataki na shiga tsakani da Hisbar ta samar.

Sai kuma daga baya wanda ake tuhumar ya yi fatali da wannan sasanci inda ya hada baki da wani mutum da ya bashi shawara ya je ya shigar da Hukumar Hisba ta Jihar Katsina Kara ta neman a hana ta sanya shi ya auri yarinyar kan dalilin wai ya tsaya takara ka da auren yarinyar ya sa a ki zabarsa.
Jami’in Hisbar ya kuma tabbatar da karbar sammacin shigar da karar da aka kawo wa hukumar tare da tabbatarwa jama’a cewa za su bi wa yarinyar hakkinta.

AMINIYA

Post masu alaƙa

NAPTIP ta ceto sama da yara 180 da ake safararsu ta hanyar ƙungiyoyin fara hula na bogi

Nafi’u ya gargaɗi Atiku ya daina sukar Tinubu da sunan ADC

Ƴansanda sun ƙara tsaurara matakan tsaro a bikin Takutaha, tare da gargaɗin masu yunkurin tada zaune tsaye.