Ƴan bindiga sun sace tsohon mai magana da yawun soji a Katsina

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun yi garkuwa da tsohon Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Sojin Najeriya, Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya, tare da matarsa a Jihar Katsina.

Wani rahoto da jaridar Daily Post ta wallafa ya nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar a yankin Matazu yayin da tsohon jami’in sojan da matarsa ke tafiya zuwa birnin Katsina.

Maharan sun tare motarsu tare da tafiya da su zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Wata majiya ta tsaro ta bayyana cewa direban motar ya samu raunin harbin bindiga lokacin harin, amma ya yi nasarar tserewa.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina da kuma rundunar sojoji ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.

Post masu alaƙa

NAPTIP ta ceto sama da yara 180 da ake safararsu ta hanyar ƙungiyoyin fara hula na bogi

Nafi’u ya gargaɗi Atiku ya daina sukar Tinubu da sunan ADC

Ƴansanda sun ƙara tsaurara matakan tsaro a bikin Takutaha, tare da gargaɗin masu yunkurin tada zaune tsaye.