NAPTIP ta ceto sama da yara 180 da ake safararsu ta hanyar ƙungiyoyin fara hula na bogi

Hukumar hana fataucin mutane ta Najeriya (NAPTIP) ta ce ta ceto yara sama da 180 da aka yi safararsu daga jihohin Kaduna, Anambra, Benue, Nasarawa da wasu wurare a ƙasar.

Hukumar ta bayyana cewa wasu ƙungiyoyin masu fataucin yara na yaudarar iyaye ta hanyar bayyana kansu a matsayin ma’aikatan ƙungiyoyin farar hula masu tallafa wa yara da ilimi, sannan su tafi da yaran da sunan ba su ilimi da tallafi.

A baya-bayan nan, an ceto wasu yara uku da aka kwaso daga Kajuru a jihar Kaduna a wani gini da ke Onitsha ta jihar Anambra, yayin da aka kuma gano wani yaro a hannun wata ma’aikaciyar lafiya.

NAPTIP ta ce wasu daga cikin yaran da aka ceto an kai su gidajen marayu inda aka rika sayar da su ga mutane da sunan ɗaukar yara reno.

Hukumar ta ce tana ci gaba da farautar masu hannu a wannan laifi domin gurfanar da su a gaban kuliya.

Post masu alaƙa

INEC ta bayyana dalilin cire wasu ’yan takarar gwamna daga jerin sunayen da ta fitar

Ƙungiyar agoya bayan  shugaba Tinubu a zargi yan Daba da hana ta kai tallafi ga marasa galihu a Bauchi .

Gwamnatin Binuwai ta rufe makarantu 2 kan tilasta wa iyaye sayen litattafai