Home » Dangote Na Shirin Faɗaɗa Matatarsa Don Zama Mafi Girma A Duniya

Dangote Na Shirin Faɗaɗa Matatarsa Don Zama Mafi Girma A Duniya

Alhaji Aliko Dangote, na shirin faɗaɗa matatar mansa domin ta riƙa tace gangar mai miliyan 1.4 a kowace rana. A halin yanzu, matatar tana tace gangar mai 650,000 a rana

by Mujahid Wada Guringawa
0 comment

Alhaji Aliko Dangote, na shirin faɗaɗa matatar mansa domin ta riƙa tace gangar mai miliyan 1.4 a kowace rana.

A halin yanzu, matatar tana tace gangar mai 650,000 a rana, amma Dangote, ya bayyana cewa suna shirin ƙara adadin cikin shekaru uku masu zuwa.

Ya bayyana haka ne yayin wani taro da manema labarai a ranar Lahadi, inda ya ce faɗaɗa aikin zai sa matatar ta zama mafi girma a duniya.

“Wannan shiri yana nuna yadda muke da cikakken shiri a Afirka da kuma dogaro da makomar Najeriya a ƙarƙashin shugabancin Bola Tinubu,” in ji shi.

Ya bayyana cewa aikin zai gudana cikin sauƙi saboda kamfanin ya riga ya gina muhimman kayan aiki da ake buƙata.

Dangote, ya ƙara da cewa wannan aikin zai taimaka wajen samar da man fetur ɗin da Afirka ke buƙata, da kuma rage shigo da mai daga ƙasashen waje.

A cewarsa aikin zai samar da guraben aiki har 65,000, inda kashi 85 cikin 100 na ma’aikatan za su kasance ’yan Najeriya.

“Manufarmu ita ce mu samar da guraben aiki da horar mutanenmu,” in ji shi.

Dangote, ya kuma sanar da cewa matatar za ta kasance a kasuwar hannun jari ta Najeriya a shekarar 2026, domin ’yan Najeriya su samu damar siyan hannayen jari.

“Muna so kowane ɗan Najeriya ya mallaki wani ɓangare na wannan matatar,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa za ake biyan kuɗin aikin daga ribar da kamfanin ke samu, tare da taimakon wasu manyan masu saka hannun jari.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?