Gwamnatin Kano ta raba kayan koyo da koyarwa ga makarantun firamare da sakandire dake fadin jihar nan. Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce samar da kayayyakin zai taimaka kwarai ga makarantun jihar nan domin farfaɗo da su. Kasancewar Inganta ilimi ne abin da Gwamnatinsa ta sa a gaba.
Engr. Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka ne a yayin bikin raba kayan, inda ya nemi waɗanda suka sami kayan karatun da su yi amfani da su ta hanyar da ta dace.
Daga bisani ya sa a kafa kwamiti don tantance malaman da suka ba da gudummawarsu wajen koyar da daliban jihar Kano cikin tsarin nan na BESDA ya ce nan da mako biyu gwamnatin za ta sa su a sahun ma’aikatan jihar kano.