Dele Momodu Ya Fice Daga PDP

DELE MOMODU

Fitaccen ɗan siyasa kuma tsohon gogaggen ɗanjaridar nan na Najeriya, Dele Momodu ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar PDP zuwa sabuwar haɗakar ADC ta an hamayya.

Domodu – wanda ya taɓa tsayawa takarar shugaban ƙasar – ya ce ya ɗauki matakin ne saboda yadda wasu da ya kira ”masu yaƙi da dimokraɗiyya” suka hana jam’iyyar numfashi.

Cikin wasiƙar ficewar tasa da ya aike wa shugaban jam’iyyar na mazaɓarsa ta Ihievbe a ƙaramar hukumar Owan ta Gabas, ranar Alhamis 17 ga watan Yuli, fitaccen ɗansiyasar ya ce dole ce ta sa ya ɗauki matakin domin maido da martabar dimokraɗiyya.

“Dalilina a bayyane yake, wasu masu yaƙi da dimokraɗiyya sun maƙure jam’iyyar daga ciki da wajen jam’iyyar”, kamar yadda wani sashe na wasiƙar ya nuna.

Post masu alaƙa

Kotu ta dage hukunci kan shari’ar datse yatsa bisa alkawarin naira miliyan 80.

Ba za mu dawo da tallafin man fetur ba —Fadar Shugaban Ƙasa

An Kashe Makiyaya 50 An Sace Shanu Sama da Dubu 2 A Kaduna — MACBAN