Jami’ar Yan Sandan Nijeriya Dake Wudil Ta Fara Binciken Masu Yunkurin Damfarar Jama’a Ta Yanar Gizo

Rahotanni na cewa jami’ar yan sandan Nijeriya dake garin Wudil, a jihar Kano ta fara gudanar bincike kan wasu batagarin mutane da ake zargi da aikewa da mutane sakonnin su bayar da kudi ta yanar gizo-gizo don basu gurbin karatu a jami’ar.

Kakakin jami’ar yan sandan Nijeriya dake Wudil, DSP Umar Musa Isah, ne ya tabbatar da fara gudanar da bincike bayan samun korafe-korafe daga wajen jama’a.

DSP Umar ya ce yanzu haka kwamandan jami’ar yan sandan, AIG Patrick Adedeji Atayero, ya bada umarnin yin bincike don gano su waye masu yunkurin yin damfarar.

Ya kara da cewa yakamata mutane su sani cewa babu wani ma’aikaci, a jami’ar da zai kira mutum ya nemi ya tura kudi kafin ba su gurbin karatu, inda ya ce form din ma ba a jami’ar ake siyar dashi ba don haka duk wanda ya tura kudi to an damfare shi.

Yaja hankalin jama’a musamman wadanda suke nemen gurbin karatu a jami’ar da su sani cewa bisa cancanta ake dauka ba ta hanyar damfara ba.

Post masu alaƙa

AIG Garba Ahmed ya bukaci daliban Sakandaren ’Yan Sanda Dawakin Kudu su zama jakadu na gari.

Babu ɗaga ƙafa tsakanin mu da masu sha da dillancin miyagun ƙwayoyi a Kano – Anti-Phone Snatching Force.

Kwamitin yaki da shaye-shaye da fadan daba na Kano ya nemi hadin kan hukumomin tsaro