Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci taron rantsar da mai shari’a, Jostis Dije Aboki, a matsayin Babbar Jojin jihar Kano a yau.
Tun a watan Maris din wannan shekarar ne ne tsohon gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, a wancan lokacin ya nada Dije Aboki a matsayin mukaddashiyar Babbar Jojin jihar.
Ita ce mace ta farko da ta riƙe muƙamin, kuma an yi bikin ne a fadar gwamnatin Kano bayan majalisar dokoki ta amince da naɗin ta a farkon watan Yuli.
Gwamnan ya ce ya naɗa ta ne “saboda kyawawan ayyukanta wajen tabbatar da adalci a harkokin shari’a”.
Ta karɓi rantsuwar kama aiki ne bisa rakiyar mijinta Abdu Aboki, wanda shi ma tsohon alƙali ne.