Cibiyar Yaƙi da Cututtuka ta Afirka (CDC) ta ce dole ne al’ummomi su taka muhimmiyar rawa wajen shawo kan annobar Ebola da ke ci gaba da yaɗuwa a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kwango (DRC).
Shugaban cibiyar, Dr Jean Kaseya, ya shaida wa BBC cewa sanya shugabannin al’umma cikin yaƙi da cutar zai taimaka wajen yaƙi da yaɗa bayanan ƙarya, gano masu ɗauke da cutar da wuri, da kuma ƙarfafa bin hanyoyin binne gawa cikin aminci.
Ya ce ana kuma shirin matsa wa da cibiyoyin gwajin Ebola da sauran ayyukan kiwon lafiya kusa da al’ummomi domin sauƙaƙa samun kulawa.
Kalaman nasa na zuwa ne yayin da adadin waɗanda aka tabbatar sun kamu da Ebola a DRC ya haura 4,000, kuma cutar ta yi sanadin mutuwar kusan mutum 1,800.
