Home » DSS Ta Gargaɗi Masu Kitsa Shirin Kafa Gwamnatin Riƙon Ƙwarya a Najeriya

DSS Ta Gargaɗi Masu Kitsa Shirin Kafa Gwamnatin Riƙon Ƙwarya a Najeriya

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya, DSS ta tabbatar da yunkurin da wasu ke yi domin samar da gwamnatin rikon kwarya a ƙasar, hukumar ta ce tana ganin hakan wani shiri ne na yi wa tsarin demokradiyya kafar ungulu da kuma son jefa kasar cikin rikici.

Wata sanarwa da hukumar DSS ɗin ta aiko wa Sashin Hausa na Muryar Amurka, mai dauke da sa hannun kakakinta Dr. Peter Afunyaya, ta ce tabbas ba za a amince da yunkurin ba, cikin tsari iri na demokradiyya dake zuwa bayan kammala zabuka cikin lumana a akasarin yankunan kasar.

Hukumar DSS ta gano wadanda ke kitsa wannan ajandar sun gudanar da taruka da dama, inda a karshe suka cimma daukar nauyin tayar da tarzoma wacce za ta haddasa zanga-zanga a manyan biranen kasar.

Ta ce hakan zai ba su damar samun ganin an ayyana dokar ta baci kuma sai su je kotu don samun hukuncin hana kaddamar da sabbin gwamnatoci a matakan tarayya da jihohi.

Saboda haka, hukumar DSS ta ce tana tare da babban kwamandan askarawan kasar a kudirinsa na tabbatar da an sami sauyin gwamnati cikin lumana bisa doron doka, inda ta ce za ta hada kai da sauran hukumomin tsaro wajen ganin an sami nasarar mika mulki cikin lumana.

Hukumar DSS ta yi gargadi ga duk masu gigin ganin sun barar da tsarin demokradiyya da su shiga taitayinsu ko su ɗanɗana kuɗarsu.

Hukumar DSS ta ja hankalin masu ruwa da tsaki a bangaren shari’a da kafafen sadarwa da kuma kungiyoyin fararen hula da su yi taka-tsantsan don kar ai amfani da su wajen hargitsa kasa.VOA

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?