Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya rantsar da tsohon shugaban ‘yan sanda Solomon Arase a matsayin shugaban hukumar ‘yan sanda na kasa.
Shugaba Buhari ya gabatar wa Majalisar tarayya sunan tsohon shugaban ‘yan sandan kamar yadda doka ta tanadar a sashin na 153 sakin layi na daya na kundin tsarin mulkin Najeriya.
An rantsar da sabon shugaban hukumar bayan kammala taron kolin na Kasa, watanni biyu bayan da Majalisar Dattijai ta tabbatar da shi.
Arase, wanda yayi aiki a matakai daban daban, ciki har da shugabantar sashin tattara bayanan manyan laifuka, sashen dake kula da tattara bayanai na hukumar ‘yan sandan Najeriya.
Ya yi ritaya a shekara ta 2016 bayan kammala wa’adin aikinsa a matsayi babban sufeton ‘yan sandan Najeriya.
Bayan Arase, shugaba Buhari ya rantsar da wasu mutane biyar a matsayin mambobin Hukumar kula da tabbatar da tsarin gwamnati wato CODE OF CONDUNCT BUREAU.