DSS ta gurfanar da mutum biyar kan zargin sace ƴan NYSC a Imo

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta Najeriya (DSS) ta gurfanar da wasu mutum biyar da ake zargi da hannu a sace wasu masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) 20 da wani farar hula a jihar Imo.

An gurfanar da waɗanda ake zargin a babbar kotun jihar Imo da ke Owerri bayan kama su a wasu samame da jami’an tsaro suka gudanar bisa bayanan sirri a jihohin Rivers da Abia.

An sace matasan masu yi wa ƙasa hidimar da farar hular ne a ranar 1 ga Oktoban 2026 a kusa da Umunoha da ke ƙaramar hukumar Mbaitoli, yayin da suke kan hanyarsu daga Ibadan zuwa sansanonin horaswa na NYSC a jihohin Abia da Akwa Ibom.

Lamarin da ya sa jami’an tsaro suka kaddamar da wani samame, inda aka ceto mutanen 21 a ranar 7 ga Oktoba daga dajin Amakohia-Ubi da ke ƙaramar hukumar Owerri ta Yamma.

Daga baya DSS ta ce ta kama mutum biyar tsakanin 10 da 14 ga Oktoba a Port Harcourt da Aba, waɗanda yanzu haka suke fuskantar shari’a.

Post masu alaƙa

An kama matashi kan zargi da safarar ’yan mata a Zamfara

Yan Sandan Kano Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Satar Mutane, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Dajin Falgore.

Iyalan jami’an yan sanda 17 sun samu tallafin Naira miliyan 7.5 a Kano.