• Home  
  • DSS ta sake gurfanar da El-Rufai kan zargin satar bayanai ta wayar Ribadu
- Babban Labari

DSS ta sake gurfanar da El-Rufai kan zargin satar bayanai ta wayar Ribadu

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan zargin sauraron kiran waya na mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA). An kawo El-Rufai kotun da misalin ƙarfe 8:55 na safiyar Litinin tare da jami’an DSS […]

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan zargin sauraron kiran waya na mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA).
An kawo El-Rufai kotun da misalin ƙarfe 8:55 na safiyar Litinin tare da jami’an DSS masu tsaurin mataki, inda suka killace harabar kotun.
Rahotanni sun ce an hana ‘yan jarida da sauran jama’a shiga kotun bayan isowarsa, lamarin da ya haifar da ɗan takaitaccen zanga-zanga.
Jagoran jam’iyyar AAC kuma ɗan gwagwarmaya, Omoyele Sowore, ya jagoranci korafin, yana cewa kotu wuri ne na jama’a kuma bai kamata a hana ‘yan ƙasa kallon shari’a ba.
Wata majiya daga hukumar ICPC ta bayyana cewa jami’an DSS sun isa ofishinsu tun ƙarfe 7:00 na safe domin ɗaukar El-Rufai zuwa kotu.
Majiyar ta ce shari’ar da ake yi ba ta ICPC ba ce, DSS ce ke jagorantar gurfanarwar.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000