DSS ta sake gurfanar da El-Rufai kan zargin satar bayanai ta wayar Ribadu

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan zargin sauraron kiran waya na mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA).
An kawo El-Rufai kotun da misalin ƙarfe 8:55 na safiyar Litinin tare da jami’an DSS masu tsaurin mataki, inda suka killace harabar kotun.
Rahotanni sun ce an hana ‘yan jarida da sauran jama’a shiga kotun bayan isowarsa, lamarin da ya haifar da ɗan takaitaccen zanga-zanga.
Jagoran jam’iyyar AAC kuma ɗan gwagwarmaya, Omoyele Sowore, ya jagoranci korafin, yana cewa kotu wuri ne na jama’a kuma bai kamata a hana ‘yan ƙasa kallon shari’a ba.
Wata majiya daga hukumar ICPC ta bayyana cewa jami’an DSS sun isa ofishinsu tun ƙarfe 7:00 na safe domin ɗaukar El-Rufai zuwa kotu.
Majiyar ta ce shari’ar da ake yi ba ta ICPC ba ce, DSS ce ke jagorantar gurfanarwar.

Post masu alaƙa

Akwai haɗa bakin ƴan cikin gida a harƙallar hukumar bogi

Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu da kashe Naira Tiriliyan 8.8 ba tare da an tanade su cikin kasafin kuɗi ba.

Gwamnatin Zamfara ta Jinjina wa shugaban NAHCON kan nasarar aikin Hajjin 2026