Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu da kashe Naira Tiriliyan 8.8 ba tare da an tanade su cikin kasafin kuɗi ba.

Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu da kashe Naira Tiriliyan 8.8 ba tare da an tanade su cikin kasafin kuɗi ba.
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC  Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin APC ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kashe kusan naira tiriliyan 8.8 na kuɗaɗin gwamnati ba tare da an tanade su a cikin kasafin kuɗi ba.
Cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu ranar Asabar, Atiku ya ce wani rahoto na Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya bayyana waɗannan kuɗin da aka kashe ba tare da cikakken bayani ba.
Ya bayyana lamarin a matsayin rashin bin ƙa’idodin tafiyar da kuɗaɗen gwamnati, tare da yin kira da a gudanar da cikakken bincike.
Ya kuma yi zargin irin wannan salon kashe kuɗi ya samo asali tun lokacin da Tinubu yake Gwamnan Jihar Legas, yana mai cewa ana amfani da waɗannan kuɗaɗen wajen ɗaukar nauyin harkokin siyasa.

Post masu alaƙa

Yan sandan Kano sun gaiyaci Aminu Warkal kan zargin nuna bindiga.

2027: Sama da mutum 10,000 sun nuna goyon bayansu ga Tinubu da Namadi a mazabar Limawa

Gwamnonin Arewa maso Gabas na yin taro a Maiduguri