Ɗan takarar mataimakin shugaban Najeriya na jam’iyyar ADC a zaɓen, Rotimi Amaechi, ya zargi hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC da shirin kama shi kafin babban zaɓen ƙasar na shekarar 2027.
A wata tattaunawa ta musamman da sashen Pidgin na BBC, tsohon minista kuma tsohon gwamnan jihar Ribas ya yi iƙirarin cewa manufar wannan shiri ita ce haifar da ruɗani da kuma hana jam’iyyarsu samun damar fafatawa a zaɓen.
BBC ta nemi jin ta bakin EFCC kan zargin, amma har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto hukumar ba ta mayar da martani ba.
Da aka matsa masa ya yi ƙarin bayani kan zargin, Amaechi ya ce baya fargaba ko shakka game da hakan ba.
“Su zo mana, ina nan ina jiransu. Ai ba wai za su ɗauke ni su tafi da ni ba ne? Manufarsu kawai ita ce su tabbatar ba mu kayar da su ba.”
Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar ke fuskantar ƙalubalen shari’a da ka iya hana ta shiga zaɓen na 2027.
A ranar 5 ga Nuwamban 2026, babbar kotun tarayya da Abuja, ta soke shugabancin jam’iyyar ADC tsagin David Mark, tare da rushe dukkan matakan da kwamitin riƙon ƙwaryar jam’iyyar na ɓangarensa suka ɗauka.
Hakan ya haɗa da zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa da ya tsayar da Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a zaɓen shekarar 2027, wanda shi kuma ya ɗauki a Amechi a matsayin ɗantakar mataimaki..
