Hukumomi a ƙasar Saudiya sun ce sun kama mutane fiye da 17,600 da suka yi yunƙiurin yin aikin hajjin bana ba tare da izini ba.
Shugaban kwamitin tsaro na aikin hajjin bana Lt. Gen. Muhammad Al Bassami ne ya bayyana hakan ga manema labarai, inda ya ce, dagacikin waɗan da aka kamadɗin, 9,509 ne suka saɓa ka’idar bizar aiki da ta zaman ƙasar.
Ya ce sun kuma kama mutum 33 da ake zargi da jagorantar mutanen ba tare da izinin hukumomin kasar ba.
Al-Bassami ya ce hukumomin ƙasar kuma sun tisa ƙeyar mutum 202,999 da suka yi yunƙurin shiga ƙasar don gudanar da aikin hajjin ba tare da izini ba.
Ƙasar ta Saudiyya tanadi cewa duk mutumin da ke zaune a ƙasar, dole ne ya nemi izinin hukumomi idan yana son gudanar da aikin hajji.