Falasdinawan da ke Gaza da Isra’ila ta shafe sama da shekara biyu tana kai wa hare-hare sun nuna jin dadi da farin ciki bayan sanar da yarjejeniyar tsagaita wuta da nufin kawo karshen yakin.
Yayin da labarin yarjejeniyar ya yadu a cikin yankin da aka kewaye, mazauna Khan Younis a kudancin Gaza sun fito tituna suna murna da fatan wannan zai zama farkon zaman lafiya daga hare-haren Isra’ila da take zaluntarsu.
“Alhamdulillah da wannan dakatar da cin zalin mu, karshen zubar da jini da kashe-kashe… duk Gaza na cikin farin ciki,” in ji Abdul Majeed Abd Rabbo, mazaunin Gaza.
Yarjejeniyar tsagaita wutar, wadda Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da ita a daren Laraba, na nuni da mataki na farko na shirin kawo karshen yakin da ya dauki shekaru biyu.
Yarjejeniyar na bukatar sakin fursunonin Isra’ila da ke hannun Falasdinawa a Gaza a madadin sakin Falasdinawa da ke hannun Isra’ila, yayin da dakarun Isra’ila za su ja da baya zuwa “layin da aka amince da shi,” a cewar Trump.
“Wannan lokaci ne da ake dauka a matsayin na tarihi, wanda Falasdinawa suka dade suna jira,” in ji Khaled Shaat, wani mazaunin Gaza.
- 2027: Atiku, Jonathan Da Obi Ba Za Su Iya Kayar Da Tinubu Ba — Kalu
- DSS Ta Saki Mahajjata 7 Da Ta Kama Da Zargin Ta’addanci
“Farin cikin da muka fara gani a tituna alama ce ta samun sauki daga kisan kiyashi da kashe-kashe.”
Gidan talabijin na Al Jazeera ya ce akwai alamun sauki ga jama’ar Gaza gaba daya. “Wannan lokaci ne na tarihi,” in ji shi.
Bayan fama da yunwa da Isra’ila ta jawo a yankin tsawon watanni, hankalin kowa ya koma kan lokacin da za a fara raba taimako, abinci da magunguna a matakin da aka gani a lokacin dakatar da fada na baya.
A daren Laraba dai, a karon farko Falasdinawa sun yi barci mai natsuwa da ba a saba da shi ba, yayin da hare-haren sama da suka zama ruwan dare suka ragu sosai.
Sai dai duk da haka, hukumar kare rayuka ta Gaza ta sanar da da Isra’ila ta kai musu wasu hare-hare bayan sanar da yarjejeniyar, ciki har da “jerin munanan hare-hare” a birnin Gaza.