Farashin litar man fetur ya karu daga 539 zuwa 617

Farashin Litar Man Fetur ya karu zuwa Naira 617 kamar yadda rahotanni suka bayyana a babban birnin tarayya, Abuja.

Gidajen man NNPC da ke Abuja sun daga farashin man daga Naira 539 zuwa Naira 617 kan kowace lita.

Ya zuwa yanzu dai ba a san dalilin da ya sa aka yi karin farashin man fetur din ba.

Amma ba zai rasa nasaba da batun da ‘yan kasuwar man fetur din suka yi na cewa farashin na iya kai wa Naira 700 kan kowace lita a baya.

Amma har yanzu Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya (NDMPRA), ba ta ce uffan kan rahoton karin man fetur din da jaridu suke wallafa cewa ta yi ba.

Post masu alaƙa

2027: ADC ta zargi Kwankwaso da yi wa Tinubu aiki

Zaɓen 2027: Rundunar yan sanda jihar Kano ta ba da tabbacin tsaro,tare da yin gargaɗi kan yada labaran ƙarya

NDLEA Ta Kama Mutane 1,860, Ta Kwace Ton 5.4 na Miyagun Ƙwayoyi a Kano.