An samu hauhawar farashin kayayyakin masarufi da kashi 22.79 a watan Yuni

Hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar nan ya ƙaru zuwa kashi 22.79 a watan Yuni daga kashi 22.41 da yake a watan Maris ɗin shekarar nan.

A wani rahoto da Hukumar Kididdiga ta ƙasa ta fitar a yau Litinin, ta ce an samu ƙaruwar ne sakamakon canjin da aka samu a farashin kayan abinci.

Rahoton ya kuma nuna cewa farashin kayan abinci ya tashi zuwa kashi 22.25 wanda ya zarce kashi 20.60 da aka samu a watan Yunin 2022.

A ranar Alhamis 13 ga watan Yuli, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ayyana dokar ta-ɓaci kan samar da abinci a matsayin martani ga hauhawar farashin abinci a ƙasar.

A ‘yan kwanakin nan, ‘yan Najeriya na kokawa kan hauhawar farashin kayan abinci, kuma a yayin da ake ci gaba da kokawa, gwamnatin tarayya ta cire tallafin man fetur, lamarin da ya ƙara jefa masu karamin karfi cikin mawuyacin hali.

Post masu alaƙa

Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Wata Mata Mai Shekaru 30 Da Katunan ATM 88

Abubuwa shida da suka sauya tun bayan zaɓen Najeriya na 2023

Kanawa mazauna Abuja sun gudanar da babban taro