DAGA: HAUWA ABUBAKAR SADIK
Shugaban ƙasar Gabon, Ali Bongo ya ce zai sake tsayawa takara a zaben da za a yi a watan Agusta, a wani mataki na ci gaba da mulki na tsawon shekaru 56 da iyalan gidan su suka yi a ƙasar.
A ranar 26 ga watan Agusta za a yi zaben shugaban ƙasa a Gabon.
Bongo mai shekaru 64, ya kasance shugaban ƙasar ta Gabon mai arzikin man fetur tsawon wa’adin mulki na shekaru bakwai har sau biyu.
Ya gaji mahaifinsa, Omar Bongo wanda ya rasu a shekara ta 2009, kuma mahaifin na sa ya jagoranci ƙasar tun daga shekarar 1967 har zuwa rasuwarsa.
Kundin tsarin mulkin Gabon bai iyakance wa’adin mulkin shugaban ƙasa ba.
A zabuƙa biyu da Ali Bongo ya samu nasara, ya fuskanci ƙalubale daga wajen ‘yan adawa inda suka yi zargin an tafka magudi.
A shekara ta 2016, lokacin da ya lashe zaben shugaban ƙasa, sai da aka yi zanga-zanga a ƙasar har aka ƙona ginin majalisar dokoki.