Gwamnatin jihar Filato ta sake ayyana dokar hana zirga-zirga ta tsawon sa’o’i ashirin da hudu a karamar hukumar Mangu, biyo bayan sake barkewar wani rikici da yayi sanadin rasa rayuka da kone-konen gidaje a yan kin.
Rikicin ya faro ne da hare-hare da ‘yan bindiga ke kai wa kan mutane a kauyuka, wanda daga bisani ya rikide zuwa na kai hari da ramuwar gayya tsakanin al’ummomin yankin da a baya ke zaman lafiya da juna.
Shugaban riko na karamar hukumar Mangu Hon. Markus Artu, ya ce harin na baya-bayan nan ya yi sanadin rasa rayuka, a saboda haka aka sanya dokar hana fita da shiga garin na Mangu.
Wannan doka ta hana yawo a karamar hukumar Mangu ita ce karo na biyu a kasa da wata guda.
Jami’in kungiyar da ke wanzar da zaman lafiya ta kasa da kasa, wato Mercy Corp, Mr. Godwin Okoko ya shawarci al’ummar yankin da su yi hakuri da juna.