Home » Gobara Ta Halaka Mutane 7 Da Lalata Kadarorin N50m A Kano

Gobara Ta Halaka Mutane 7 Da Lalata Kadarorin N50m A Kano

by Mujahid Wada Guringawa
0 comment

 

Mutane bakwai ne suka rasa rayukansu yayin da kadarori na sama da Naira miliyan 50 suka salwanta sanadiyyar gobarar a cikin watan Fabrairun 2025 a Jihar Kano.

Kakakin hukumar kashe gobara, Saminu Yusif Abdullahi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a jihar.

Ya ce, a cikin watan Fabrairu, 2025, hukumar kashe gobara ta jihar ta samu jimillar kiraye-kirayen lambar wayar kashe gobara 77, da lambar kiran neman ceto 11 da kuma ƙararrakin gobara na ƙarya uku.

“Kimanin kadarori da gobara ta lalata a cikin watan Fabrairu sun kai darajar kuɗi N50,318,000 yayin da ƙiyasin kadarorin da jami’an kashe gobara na jihar suka ceto sun kai N180,318,000.

“Rayukan mutane bakwai ne suka salwanta sakamakon wata gobara da ta tashi yayin da kuma aka ceto rayukan mutum bakwai.”

Hukumar ta yi kira ga jama’a da su riƙa kula da wuta cikin kulawa domin gujewa afkuwar gobara yayin da aka shawarci masu ababen hawa da su riƙa tuka mota cikin kulawa tare da bin dokar hanya musamman a lokacin da suke tafiya kan manyan hanyoyi domin guje wa haɗurran mota.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?