Daga: Safiyanu Haruna Kutama
Tashin wata mummunar gobara yayi sanadiyyar konewar shaguna 103, na kayan abinci a kasuwar Gusau dake jihar Zamfara.
Rahotanni sun shaida cewa kayan abincin da suka kone sun kasance masu saurin lalacewa.
Zuwa yanzu ba’a kai ga tantance dalilin tashin gobarar ba, amma daya daga cikin mutanen da suka kashe wutar ya shaidawa Daily trust, cewa wutar lantarki nada alaka ta kusa da tashin gobarar saboda an samu faruwar lamarin jim kadan bayan kawo wuta a kasuwar.
Wutar ta kama da misalin karfe 10:30, na daren lahadin data gabata, wanda ta dauki lokaci mai tsayi tana ci kafin a samu nasarar kashe ta da karfe 2 na daren.
- Anya Gwamnati Najeriya za ta iya kula da shirin yaƙi da cutar HIV
- Jam’iyyar NNPP Ta Dakatar Da Sanata Kawu A Kano
Shugaban kungiyar masu sayar da kayan abincin Alhaji Inusa Saminu ya shaida wa jaridar ta Daily Trust cewa, tashin gobarar ya ta’azzara wanda har yanzu ba’a san adadin kudaden da akayi asara ba.
Yace rashin isowar jami’an kashe gobara akan lokaci ya kara janyo karuwar asarar da suka yi.