• Home  
  • Sojoji Sun Gano Maboyar Bello Turji 
- Babban Labari - Labarai

Sojoji Sun Gano Maboyar Bello Turji 

Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya ta bakin Babban Jami’in Ayyukanta Manjo-Janar Emeka Onumajuru, ta bayyana cewa saura kiris su gama da jagoran ’yan ta’addan da ya addabi yankin Arewa maso Yamma Kacalla Bello Turji.

Manjo-Janar Emeka Onumajuru ya bayyana cewa sojojin suna kan bibiyar motsin Bello Turji, kuma sun gano inda yake, amma bai yi ƙarin bayani ba.

“Babu wani kwan-gaba-kwan-baya a wurin sojoji kan maganar Bello Turji, mun gano inda maɓoyarsa take,” in ji Janar Emeka.

Ya ci gaba da cewa a halin yanzu sojoji sun riga sun rutsa Turji a maɓoyarsa, babu inda zai iya motsawa ya je, saboda tsoro

Ya bayyana haka ne a safiyar Litinin yana mai cewa kwanakon Turji sun kusa karewa.

Janar din ya bayyana haka ne a yayin hirar da gidan talabijin na Channels ya yi da shi a ranar.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai