Gobara ta yi ajalin ɗalibai 16 a Kenya

Ɗalibai 16 sun mutu sakamakon wata gobara da ta tashi a makarantar kwana da ke Gilgil a Kenya, kamar yadda wani ɗansanda ya shaida wa manema labarai.

Wasu ɗalibai 74 kuma suna samun kulawa a asibiti bayan raunin da suka ji.

Gobarar da ta faru a makarantar ƴanmata ta Utumishi ta soma ne da sanyin safiyar yau Alhamis lokacin da ɗaliban suke barci, in ji ƙungiyar agaji ta Red Cross a Kenya da kuma ƴansanda.

Ƴansanda sun ce ana aikin ceto sai dai zuwa yanzu hukumomi ba su gano musabbabin gobarar ba.

Ƙungiyar Red Cross a Kenya ta ce masu bayar da agajin gaggawa na wajen domin ba da tasu gudunmawar.

A yayin da yake magana da iyayen ɗalibai da sauran mutanen da suka taru a wajen makarantar, babban jami’in ƴansanda Masoud Mwinyi ya ce lamarin abin tashin hankali ne.

Dama a kan samu tashin gobara a makarantun kwana a Kenya inda a shekarun baya-bayan nan lamari ya janyo mutuwar mutane.

Post masu alaƙa

NAPTIP ta ceto sama da yara 180 da ake safararsu ta hanyar ƙungiyoyin fara hula na bogi

Nafi’u ya gargaɗi Atiku ya daina sukar Tinubu da sunan ADC

Ƴansanda sun ƙara tsaurara matakan tsaro a bikin Takutaha, tare da gargaɗin masu yunkurin tada zaune tsaye.