Sanata Omo-Agege ya fice daga APC

Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ovie Omo-Agege ya fice daga Jam’iyyar APC mai mulki.

Cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara ka harkar labarai, Sunday Areh ya fitar, Sanata Omo-Agege ya ce ya ɗauki matakin ne bayan tuntuɓa da ya yi da makusantansa a siyasa da kuma magoya bayansa, bugu da ƙari kuma abubuwan baya-baya da suka faru a jam’iyyar reshen jihar Delta.

Tsohon ɗanmajalisar ya ce ya fi dacewa ya nemi cika burinsa na siyasa da muradan da yake da shi ga al’ummar mazaɓarsa a wata jam’iyyar inda ya ƙara da cewa ba zai ci gaba da kasancewa a jam’iyyar da ba zai iya samar da ci gaba ga mutanensa ba.

Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito Omo-Agege yana gode wa APC bisa damar da ta ba shi na riƙe muƙamin mataimakin shugaban majalisar dattawa a majalisa ta tara inda kuma ya ce yana yi wa jam’iyyar fatan alheri.

Post masu alaƙa

INEC ta bayyana dalilin cire wasu ’yan takarar gwamna daga jerin sunayen da ta fitar

Ƙungiyar agoya bayan  shugaba Tinubu a zargi yan Daba da hana ta kai tallafi ga marasa galihu a Bauchi .

Gwamnatin Binuwai ta rufe makarantu 2 kan tilasta wa iyaye sayen litattafai