Gobe Litinin Za A Yi Jjana’izar Marigayi Aminu Ɗantata A Madina

Babban sakataren marigayi Alhaji Aminu Dantata, Mustapha Abdullahi Junaid ya ce shirye-shirye sun kammala domin gudanar da jana’iza tare da binne gawar marigayin a garin Madina.

Mustapha ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook, inda ya rubuta cewa, “Alhamdulillah an samu amincewar (hukumomi), za a ɗauki Aminu Alhassan Ɗantata daga Abu Dhabi zuwa Madina. Za a yi jana’iza gobe da safe in sha Allah.”

A safiyar jiya Asabar ne da attajirin ɗankasuwar ya rasu a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, amma iyalansa suka jinkirta binne shi domin a cewarsu, suna su ne su cika masa burinsa na kasancewar a binne a garin na Madina.

An dai gudanar masa da sallar da gawa ba ta kusa a jihar Kano, wanda Sheikh Ibrahim Khalil ya jagoranta.

Post masu alaƙa

Yar Najeriya ta kammala jami’ar Burtaniya da daraja ta daya (1st Class) a ilimin kimiyar samar da manhajar kasuwancin zamani.

Gwamnati ta buƙaci jama’a su guji taɓa kumfar da ta ɓulla a hanyar Kaduna-Abuja

A riƙa yi wa masu shirin aure gwajin miyagun ƙwayoyi :- Buba Marwa