Gwamnati ta buƙaci jama’a su guji taɓa kumfar da ta ɓulla a hanyar Kaduna-Abuja

Gwamnatin Najeriya ta gargadi jama’a da su guji taɓa wata farar kumfa da ta bayyana a gefen hanyar Kaduna zuwa Abuja, bayan zargin cewa wata mota mai ɗaukar kaya ta zubar da wani sinadari a wurin.

Hukumar Kula da Ka’idojin Muhalli ta ƙasar, NESREA, ta ce ta fara bincike domin gano musabbabin samuwar kumfar.

A wata sanarwa da mataimakiyar daraktan yaɗa labarai na hukumar, Nwamaka Ejiofor, ta fitar, ta ce jami’an NESREA daga ofishin Kaduna, sun ziyarci wurin domin gudanar da bincike.

Ta ce tawagar ta gana da kwamandan ƴan sanda na Jere, ACP Sani Zubairu da babban jami’an hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC), da kuma shugabannin al’ummar yankin.

Binciken farko ya nuna cewa wata babbar mota ce ta yi hatsari a wurin, wanda ya jawo zubar da kayan da take ɗauke da su.

NESREA ta ce ta tattara bayanai daga jami’an gwamnati da mazauna yankin, sannan ta ɗauki samfurin kumfar, ƙasar wurin da kuma ruwan wani rafi da ke kusa domin a yi gwajin dakin bincike.

Hukumar ta yi kira ga jama’a da su guji kusantar kumfar da ruwan da ke kusa da wurin da kuma ƙasar da ke kewaye da shi har sai an kammala binciken, domin kauce wa yiwuwar haɗuwa da wani abu mai illa ga lafiya.

Post masu alaƙa

Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama wanda ake zargi da damfarar mutane da cewa shi babban jami’in Dan sandan ne.

Hisbah ta fara horas da sabbin jami’anta a Jigawa

Dan KAROTA da direba ya buge ya gudu Nasiru Abdullahi Mai Jihadi ya rasu ya bar mata 2 da ‘ya’ya 12.