Home » kwamitin kwashe shara ta jihar Kano ya sanar da shiga matakin karshe na kammala aikinsa

kwamitin kwashe shara ta jihar Kano ya sanar da shiga matakin karshe na kammala aikinsa

by Anas Dansalma
0 comment
kwamitin kwashe shara ta jihar Kano ya sanar da shiga matakin karshe na kammala aikinsa

Shugaban kwamitin kwashe shara na jihar Kano Amb. Alhaji Ahmadu Haruna Zago ya bayyana cewa nan da kwanaki biyu masu zuwa kwamitinsa zai kammala aikinsa, wanda a yanzu aikin nasu na kwashe sharar yana matakin karshe.

Ɗan Zagon ya bayyana hakan ne lokacin da ake kammala kwashe sharar dake Shahuci daidai police station.

Ya ƙara da cewa ‘’Tun da gwamna ya dora mana wannan aiki muke shiga lungu da sako na jihar kano domin kwashe tarin sharar da ta addabi al’umma Kuma masha Allah kwalliya ta biya kudin sabulu”.

Amb. Ahmadu Haruna zago ya yaba wa daukacin al’ummar jihar kano bisa hadin kai da goyon bayan da suka bai wa kwamitinsu wajen kwashe shara a birnin kano, Inda Kuma ya yi kira a gare su da su bai wa dukkanin ayyukan da gwamnatin Abba Kabir Yusuf za ta yi goyon baya domin ciyar da jihar Kano baba.

Shi ma a nasa jawabin daraktan ayyuka na hukumar kwashe sharar jihar Kanon, Alhaji Sha’aya’u Abdulkadir Jibrin ya ce rashin isassun kayan aiki ne ya hana su kwashe sharar tuntuni.

Amma ya yabawa wannan tsari da gwamnatin jihar kano ta bullo da shi wanda a cewarsa zai matukar taimakawa wajen inganta lafiya da rayuwar al’umma kano

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?