Kotun kolin Najeriya ta tabbatar da hukuncin kwace kadarorin Godwin Emefiele

Kotun koli Najeriya ta tabbatar da hukuncin ƙwace kadarori bakwai da kuɗaɗe sama da dala miliyan biyu da ake dangantawa da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, tare mallakawa gwamnatin tarayya.

Kotun ta yanke hukuncin ne bayan ta soke hukuncin Kotun daukaka kara, tare da amincewa da hukuncin babbar kotun tarayya da ke Legas, wadda ta ce akwai hujjojin da ke nuna cewa an mallaki kadarorin ne ta haramtacciyar hanya.

Tun da farko dai hukumar EFCC ce ta nemi kotu ta ba da umarnin ƙwace kadarorin, bayan binciken da ta gudanar kan yadda aka mallake su.

Kadarorin da aka ƙwace sun haɗa da gidaje da filaye a Legas, wani katafaren ginin masana’antu da ake ginawa a Jihar Delta, kuɗi dala miliyan biyu da dubu 45, da kuma takardun hannun jari na wani kamfani.

 

Post masu alaƙa

Dalibai huɗu za su wakilci Najeriya a gasar Spelling Bee ta Duniya a China

Babandede Ya Taya Shettima Murnar Sake Samun Takarar Mataimakin Shugaban Kasa

Ban taɓa haɗuwa da Adeyemi ba — Gbajabiamila