• Home  
  • Gwamnan Jihar Kebbi Nasir Idris Ya Ce Ba A Biya Kudin Fansa Ba Kafin Ceto Daliban Da Aka Sace
- Babban Labari - Labarai

Gwamnan Jihar Kebbi Nasir Idris Ya Ce Ba A Biya Kudin Fansa Ba Kafin Ceto Daliban Da Aka Sace

Gwamnan Jihar Kebbi Nasir Idris ya ce ɗaliban jihar da aka kuɓutar daga hannun ƴanbindiga na cikin ƙoshin lafiya. A wani taron manema labarai da gwamnan ya gabatar a fadar gwamnatin jihar da ke Birnin Kebbi jim kaɗan bayan sanar da sakin ɗaliban, gwamnan ya gode wa shugaba Tinubu da sauran jami’an tsaro da suka […]

Gwamnan Jihar Kebbi Nasir Idris ya ce ɗaliban jihar da aka kuɓutar daga hannun ƴanbindiga na cikin ƙoshin lafiya.

A wani taron manema labarai da gwamnan ya gabatar a fadar gwamnatin jihar da ke Birnin Kebbi jim kaɗan bayan sanar da sakin ɗaliban, gwamnan ya gode wa shugaba Tinubu da sauran jami’an tsaro da suka taimaka wajen kuɓutar da ɗaliban.

”Daga bayanan da muke da su yanzu haka yaran suna kan hanya, kuma suna cikin ƙoshin lafiya, lafiyar kalau aka same su”, in ji shi.

Gwamna Nasir Idris ya kuma ce ba a biya ko sisin kwabo ba a matsayin kuɗin fansa, domin karɓo ɗaliban 24.

”Mun bincika koda an biya kuɗin fansa ne, kuma daga bayanan da muka samu ba a biya kuɗin fansa ba, mu dai gwamnatin jihar Kebbi ba mu biya ko kwabo ba, kuma su ma jami’an da suke je karɓo su sun ce ba su je da kuɗi ba”, in ji shi.

Gwamnan ya kuma ce gobe za a damƙa ɗaliban a hannun iyayensu.

A makon da ya gabata ne aka sace ɗaliban a makarantar sakandiren ƴanmata da ke Maga a jihar.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai