• Home  
  • NOA Ta Kaddamar Da Kwamitin Samar DA Darasin Kishin Kasa A Jadawalin Karatun Jami’o’in Nijeriya
- Babban Labari - Labarai

NOA Ta Kaddamar Da Kwamitin Samar DA Darasin Kishin Kasa A Jadawalin Karatun Jami’o’in Nijeriya

Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa NOA ta kaddamar da kwamitin hadin gwiwa da hukumar dake kula da jami’o’in Nijeriya, NUC, don shigar da darasin sanin kasa da kishinta, a cikin jadawalin karatun jami’o’in fadin kasar. Jami’in yada labaran hukumar NOA, Bala Musa , ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa […]

Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa NOA ta kaddamar da kwamitin hadin gwiwa da hukumar dake kula da jami’o’in Nijeriya, NUC, don shigar da darasin sanin kasa da kishinta, a cikin jadawalin karatun jami’o’in fadin kasar.

Jami’in yada labaran hukumar NOA, Bala Musa , ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai.

Sanarwar ta kara da cewa shugaban hukumar NOA, Mallam Lanre Issa-Onilu, ya ce shirin wani bangare ne na aikin farfado da aikin kimiyar Nijeriya da manufar tsarin da zai koyar da matasa dabi’u nagari da zama nagartattun yan kasa.

Anata bangaren shugabar tawagar jami’o’i ta kasa NUC, Florence Uju Onuoha, ta yabawa kwamitin tarayyar kan amince da shirin, inda ta tabbatar da cewa hakan zai taimaka wajen gina al’umma masu kishin kasa da kuma karfafa zaman lafiya.

A karshe sanarwar ta ce tuni shirye-shirye sun yi nisa don aiwatar da shirin.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai