Home » Gwamnan jihar Zamfara ya kori manyan sakatarorin ma’aikatu da wasu hakimai

Gwamnan jihar Zamfara ya kori manyan sakatarorin ma’aikatu da wasu hakimai

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment
Gwamnan jihar Zamfara ya kori man sakatarorin ma'aikatu da wasu hakimai

Gwamnan jihar Zamfara, Daula Lawal Dare, ya kori duk manyan sakatarorin ma’aikatun gwamnatin jihar Zamfara.

Fatattakar ba ta tsaya ga manyan sakatarori ba, har da duka wani hakimi ko dagaci da tsohon gwamna Bello Matawalle ya naɗa.

Gwamnatin jihar ta ce matakin na daya daga cikin sauye-sauyen da ta fara yi na gyara yadda Matawalle ya yi wuju-wuju da dukiyar jihar.

Sakataren gwamnatin jihar, Abubakar Nakwada, a wata ganawa da manema labarai da ya yi a Gusau ya ce gwamnatin da ta shude ta yi barna da marar misaltuwa da ya shafi tattalin arzikin jihar.

Sakataren ya kara da cewa dukkan gundumomin da aka kirkira a watan Disambar shekarar 2022 an rusa su, sannan kuma duk wani babban sakatare da aka naɗa da aka ɗora bayan babban zaben 2023, shima ya tattara komatsansa ya kara ga ba.

Sannan ya zargi gwamnatin Matawalle da kashe Naira biliyan 50 wajen gudanar da ayyuka a gidan gwamnati wadanda ba su da wani tasiri ga ci gaba a jihar.

A cewarsa ko da cikin gidan gwamnatin ma, babu abin da mutum zai gani na waɗancan kuɗaɗe.

Ga batun motoci na alfarma da tsohuwar gwamnatin ta kashe biliyoyin nairori wajen siyansu kuma ko ɗaya sabuwar gwamnati ba.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?