Hukumar Shige da Fice ta Kasa (NIS) karkashin jagorancin Kwanturola Janar Wuraola Adepoju ta daukaka darajar jami’anta kusan 7,000.
Jawqbin hakan, na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun sakataren hukumar, Alhaji Jafaru Ahmed.
A jawabinta ga Jami’ai da Ma’aikatan Hukumar a lokacin faretin wata-wata, hukumar ta bukaci da su fifita martabar aikin fiye da bukatun kashin kansu domin hukumar na daya daga cikin manyan hukumomin da alhakin kare dukiyoyin al’umma ya rataya a wuyansu.
Sannan ta yi alkawarin ba da fifikon jin dadin ma’aikata, tare da shan alwashin cewa daga yanzu dole ne a yi wa manyan jami’ai karin girma domin abin takaici ne ganin yadda wasu tsofaffin jami’ai suka dade a mataki daya.