Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya gabatar wa majalisar dokokin jihar Kano ƙwarya-ƙwaryar kasafin kuɗi na fiye da Naira biliyan 58.
Shugaban majalisar Jibril Isma’il Falgore ne ya bayyana hakan yayin da ya ke karanta wasiƙar da gwamnan ya aike wa majalisar yayin zamanta na yau Litinin.
Ta cikin wasiƙar, gwamna, Abba Kabir Yusuf, ya buƙaci majalisar ta sahale masa kashe fiye da Naira biliyan 58 da miliyan 191 da dubu 535.