Home » Gwamnan Kano Ya Gana da Zababben Shugaban Kasa Tinubu a Abuja

Gwamnan Kano Ya Gana da Zababben Shugaban Kasa Tinubu a Abuja

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment
Gwamnan Kano Ya Gana da Zababben Shugaban Kasa Tinubu a Abuja

Shugaban kasa mai jiran gado, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, ya gana da Gwamnan Jihar Kano mai barin gado, Abdullahi Umar Ganduje a gidansa na Defense House da ke Abuja.

Da yammacin jiya Asabar ne Ganduje ya shiga sahun waɗanda suka taro Asiwaju Tinubu lokacin da ya sauka Abuja daga ƙasar Faransa.

Bayan an isa gida kuma sun yi ganawar sirri tsakaninsu.

Ganawar dai ba ta rasa nasaba da ƙorafin da Ganduje yake da shi game da ganawar Asiwaju Tinubu da tsohon gwamnan Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso a birnin Paris.

A baya-bayan nan dai aka ji wani sautin hirar wayar tarho na yawo inda Ganduje ke kukan zaɓaɓɓen shugaban ƙasar bai kyauta masa ba da ya yi wannan tattaunawar.

Kawo yanzu dai Ganduje bai bayyana wa manema labarai matsayar da suka cimma da Asiwaju Tinubu ba.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?