Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya yaba wa wani matashi mai suna, Yusuf Sulaiman Sumaila, saboda ya mayar da albashin da aka tura wa mahaifinsa wanda ya rasu tun a watan Oktoban shekarar da ta gabata.
Mai bai wa gwamnan shawara na musamman kan kafofin yaɗa labarai ta intanet, Abdullahi Ibrahim ne ya bayyana hakan a shafinsa na X wanda aka fi sani da Twitter.
Watanni goma sha ɗaya ke nan da rasuwar mahaifin Yusuf Sulaiman Sumaila amma gwamnatin Kano ta ci gaba da tura masa albashi har zuwa watan Agustan wannan shekara da muke ciki.
Bayan Yusuf ya lura da hakan ne ya mayar wa gwamnatin Kano albashin da aka riga a tura wa mahaifin nasa wanda ya kama Naira dubu ɗari 3 da 28 da 115 da kwabo 75. (328, 115, 75)
Bayan Yusuf ya mayar da waɗannan kuɗaɗe ne kuma, gwamnan jihar Kano ya buƙaci ganawa da shi domin miƙa masa godiyarsa bisa gaskiyar da ya nuna tare da neman sauran matasa su yi koyi da shi.